A karo na biyu cikin kwanaki, wasu ‘yan uwa tara ne suka mutu a wani lamari mai abin ban mamaki a jihar Kogi.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a garin Nagazi da ke karkashin karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi
KARANTA WANNAN LABARIN: Uwar Jam’iyyar PDP Ta Ƙasa Ta Tsoma Baki a Rikicin Reshen Jihar Ogun
Wannan lamari na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan uwa guda hudu sun mutu a karamar hukumar Mopa-Muro dake jihar Kogi a karshen mako.
DAILY POST ta tattaro da yammacin ranar Litinin cewa lamarin da ya faru a Nagazi inda aka ga wasu ‘yan uwa guda biyar suna mutuwa a wuri guda kafin a garzaya da saran hudu zuwa asibiti.
Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa sauran hudun daga baya sun mutu a wani asibiti da ba a bayyana ba a yankin.
A cewar wata majiya mai tushe, wacce ba ta so a ambaci sunanta ba, an kama mahaifin wadanda abin ya shafa yayin da mahaifiyar su ke ci gaba da karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Ya ce har yanzu ba su san ainihin musabbabin mutuwar ba saboda suna zargin gubar abinci ko kuma harin tsafi.
Duk kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi William Ovye Aya ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Bai dauki waya ko amsa sakon da aka aika a layukan wayarsa ba.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa idan za’a iya tunawa wasu mutane biyar sun rasa rayukansu a watan Agustan 2022 bayan cin abincin garin rogo da aka shirya a gidansu da ke Usugnwe-Okaito, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi.
A wani labarin kuma, Buhari Ya Binne Ilimi, Za Mu Yi Jana’izar Sa – NANSK
Kungiyar daliban Najeriya reshen shiyyar Kudu maso Yamma, ta ce a shirye ta ke ta gudanar da jana’izar ilimin al’umma, inda ta zargi shugaban kasa, Muhammadu Buhari da binne ilimin al’umma a kasar.
Daliban, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun ko-odinetan su, kuma kakakin su, Adegboye Olatunji da Awoyinfa Opeoluwa,wanda kuma suka akawa da jaridar PUNCH a ranar Litinin, sun ce nan da kwanaki masu zuwa za su sake afkawa kan tituna.