Wata babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama, a Abuja ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar Juma’a, domin yanke hukunci kan karar da bangaren gwamna Abdullahi Ganduje na jam’iyyar (APC) suka shigar.
A zaman kotun na ranar Alhamis, Mai shari’a Hamzat Muazu, ya ce an dage shari’ar da aka sanya don yanke hukunci kan bukatar da wasu bangarorin biyu suka shigar na neman a yi watsi da hukuncin da aka yi tun farko a karar da suke bukata a saura.
Daga nan ne kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar Juma’a domin yanke hukunci kan bukatar a yi watsi da karar.
A halin da ake ciki, tun da farko Abdullahi Ganduje ya bukaci kotun da ta yi watsi da hukuncin da ta yanke ranar 30 ga watan Nuwamba, domin tabbatar da taron mazabukan da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya gudanar a Kano.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, a baya kotun ta yanke hukunci bisa karar da tsagin shekarau suka shigar, inda ta ayyana zaben su a matsayin halastacce.
Sai dai tsagin Ganduje, Sun yi tir da cewa ba a saurare su daga fara shari’ar ba don haka a ajiye maganar a gefe.
Sai dai kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Janairu bisa wannan bukata ta musamman.