Gobara ta kone wani kamfani Alibert Furniture dake kan hanyar Murtala Mohammed a cikin birnin Kano.
Majiyar Solacebase ta ruwaito cewa, shedun gani da ido sun ce gobarar da ta tashi da sanyin safiyar ranar Litinin, ta lalata kamfanin daura da Kano Club, da makwabciyar kamfanin Fridabs Solacebase Communications Ltd, kamfanin buga jaridar Solacebase ta yanar gizo gaba daya.
Tasirin gobarar ta shafi sashin ofishin Solacebase.
An garzaya da jami’an tsaro biyu na kamfanin da suka samu raunuka zuwa asibiti, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.
Ko da yake har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, amma shaidu na alakanta lamarin da matsalar wutar lantarki daga taransfomar kamfanin.
Ko da yake jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar, har yanzu wutar na ci gaba da ruruwa.
Cikakkun bayanai daga baya…