Mutane 4 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wata guguwar iska ta yi barna a unguwar Hashimeri da ke Damaturu a jihar Yobe.
Haka kuma, a kalla gidaje 35 ne suka ruguje yayin faruwar lamarin.
Guguwar wadda ta fara da karfe 11:00 na daren ranar Asabar da ta wuce tsawon mintuna 20 kacal, ta lalata gidaje a kauyukan da aka gina da bulo.
Sauran wuraren da abin ya shafa sun hada da unguwannin Nayinawa da Abacha na babban birnin jihar.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Muhammad Goje, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Ya ce ba a samu rahoton mutuwar mutane 17 ba, kuma an kwashe mutane 17 suna karbar magani kyauta a asibitin kwararru na jihar da ke Damaturu.
Hakazalika, mazauna Damaturu sun koka kan yadda lamarin ya kasance kusan shekara-shekara don haka sun yi kira ga gwamnati da ta samar da mafita mai dorewa kan lamarin.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da guguwar iska ta yi ta addabar jihar a baya-bayan nan.
Dimokuradiyya ta rawaito, A ranar 10 ga watan Mayu, wata mahaukaciyar guguwa mai karfin gaske ta kashe mutane biyar a Damaturu. An tattaro cewa guguwar na tare da wata iska mai karfi, wadda ta ruguza gidaje tare da lalata kadarori da dama.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta tabbatar da cewa mutane biyar ne suka mutu yayin da wasu 42 suka samu raunuka daban-daban a lokacin guguwar.
Daraktan ceto a SEMA, Baba Jalo, ya bayyana cewa wadanda suka mutu sun mutu ne a gine-ginen da suka ruguje a lokacin guguwar.
Ya ce kaddarorin da guguwar ta lalata a sassa daban-daban na birnin, da suka hada da Maisadari, Nayinawa, da kuma Pompomari, ya danganta iska mai karfi da tasirin yanayi.