Jam’iyyar PRP ta bukaci sabon gwamnan jihar Kano da aka rantsar, Abba Kabir Yusif, da ya yi amfani da ofishinsa wajen fifita muradun al’ummar jihar, ba don biyan bukatun kansa ba.
Mambobin dandalin dan takarar jam’iyyar PRP ta Kano a 2023 ne suka yi wannan kiran a wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin din nan.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Jam’iyyar ta kuma gargadi gwamnan kan kada wani mutum ko kungiya ko wani son rai na siyasa ta sa shi yin wani abu.
KARANTA WANNAN Ba Ganduje Ne Ya Dauki Nauyin Takarata Ba — Dan Takarar Gwamna PRP
Sakamakon haka, Dandalin ya bayyana cewa, “Zabe shi ne hanya daya tilo da doka ta amince da ita wajen samar da shugabanni a karkashin mulkin Dimokradiyya a Najeriya; kuma dole ne a samu mai nasara da wanda bai yi nasara ba.
“Muna kira ga sabuwar gwamnati da ta fifita maslahar kasa baki daya a sama da kowane mutum ko muradin ‘yan uwantaka ko ra’ayi na bangaranci.
Dandalin ya ce, “Mu farfado da bangaren ilimi da ya lalace, da inganta harkokin kiwon lafiyar jama’a, da samar da manufofi da tsare-tsare da za su bunkasa noma, kasuwanci da masana’antu, samar da ayyukan yi da kawar da fatara.”
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Jam’iyyar ta taya gwamnan da sauran ‘yan takarar da suka ci zabe a karkashin jam’iyyun siyasa daban-daban murnar nasarar da suka samu.
A Wani Labarin Kuma Yadda Malami Ya Yi Sumar Da Dalibar Sa Da Duka
A wani abin da aka bayyana a matsayin nuna rashin tausayi na wani malami wajen ladabtar da dalibai, wata dalibar SS3 da ke makarantar Government Girls Science Secondary School (GGSSS) Kuje, Christabel Mimi Henry, a yammacin ranar Juma’a ta sha dukan tsiya daya sumar da’ita daga malaminta wanda aka bayyana shi da suna David.
A cewar mahaifin Christabel, Mista Henry Iortim, daya daga cikin daliban ya kira shi inda ya bukaci ya ziyarce shi a babban asibitin Kuje, saboda an garzaya da ‘yarsa don ganin ta farfado daga suman data yi, bayan da aka yi mata dukan tsiya da Sanda daga malaminta.