Wata mata da har yanzu ba a tantance ko tana dauke da cutar kanjamau ta HIV ba, ta ce tana hada jininta a cikin ruwan zobon da take sayarwa domin akara samun wasu mutanen da cutar ta kama.
Matar ta bayyana hakan ne a wani shirin gidan rediyon Wazobia FM, MarketRunz a daren Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Wani Babban Filin Wasanni Ya Rufta, Ya Halaka Mutum Uku a Najeriya
Mai gabatar da shirin ya nemi masu sauraro su kira su shaida abin da suke yi a kasuwa wanda mutane ba su sani ba da kuma abin da ba sa alfahari dashi.
Mai sayar da zobon ta ce, “Na je asibiti wata shida da suka wuce, sai aka ce mini ina da cutar kanjamau wato HIV.
“Ba ni da kuɗin magani don haka na yanke shawarar cewa ba zan mutu ni kaɗai ba. Na fara hada jinina da zobo da nake yi in sayarwa da mutane don suma suka mu don mukara yawa.
“Ina zukar jinina da sirinji in hada shi a zobo. A da ni ma’aikaciyar jinya ce amma da aka tabbatar min da ina da cutar kanjamau, sai na daina zuwa Aiki.
“Ban ji dadin abin da na yi ba amma ina farin ciki cewa ba zan mutu ni kadai ba.”
“Na yi wata shida yanzu ina addu’ar Allah ya gafarta min.”
A wani labarin kuma, Ba ma Amfani Da POS Wurin Amsan Kudin Tara— Hukumar FRSC
Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa, ta bayyana cewa, Ba ta Amfani da na’urar cire kudin tafida gidanka wato POS Don Karbar Biyan Tarar masu ababen hawa da suka karya ka’idojin hanya.
Jami’in kula da ilimantar da jama’a na hukumar FRSC, Bisi Kazeem ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa a da ya fitar ranar Laraba.