Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta tabbatar da cafke wata uwar ‘ya’ya biyu mai suna Misis Charity Upev bisa zarginta da lakada wa yaronta mai suna Fanen dan shekara 10 da haihuwa duka inda ta kashe shi har lahira sakamakon wani nama da ya bata.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 23 ga watan Janairu, 2023, a kan titin Abu King Shuluwa, kusa da kasuwar duniya, bayan Deeper life camp a Makurdi, babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Balogun a jihar Legas
An tattaro cewa an kama wadda ake zargin ne bayan da makwabtanta suka kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda ‘E Division’ dake jihar.
Wata majiya a unguwar da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa mutuwar marigayin kusan ta haifar da zanga-zangar fusata da matasan yankin da suka so nuna fushinsu a kan wanda ake zargin amma jami’an ‘yan sanda sun yi gaggawar shiga cikin lamarin.
Majiyar ta shaida wa Jaridar Vanguard cewa, “An ce matar ta yi wa yaron dukan tsiya da safiyar ranar Lahadi bisa zarginsa da dauke wani nama a cikin tukunyar miyar ta, amma da yamma sai yaron ya fara amai da abin da ake zargin jini ne.
“An garzaya da shi Asibiti, jim kadan bayan rasuwarsa, don haka kowa na cewa yaron da ke a gidan matar, tabbas ya samu zubar jini a ciki wanda ya kai ga mutuwarsa.
“Duk da cewa wannan hasashe ne saboda har yanzu ba a gama binciken gawar ba kan abin da ya yi sanadin mutuwar ba, amma abin da ake dauka a unguwar shi ne ya mutu ne sakamakon duka da aka yi masa a safiyar ranar.”
Kakakin rundunar SP Catherine Anene, wadda ta tabbatar da mutuwar yaron mai shekaru 10, ta ce an kama wanda ake zargin.
“A ranar 23 ga watan Janairun 2023 da misalin karfe 5 na yamma, an samu rahoton kisan gilla a ofishin ‘yan sanda na ‘E’ dake Makurdi, nan take aka tura tawagar jami’an tsaro,” in ji sanarwar.
“Bincike na farko ya nuna cewa marigayin, Fanen Yange, mai shekaru 10 a Duniya dake Makurdi mahaifiyarsa, Misis Upev tana zargin sa da satar nama a cikin tukunyar, kuma ta yi masa dukan tsiya da sanyin safiyar ranar wanda yayi sanadin mutuwar sa”.
Kakakin ‘yan sanda ta bayyana cewa, an ajiye gawar yaron a dakin ajiyar gawa na asibitin Bishop Murray na Makurdi inda ake jiran a gudanar da bincike a kan lamarin.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Fara Ziyarar Aiki Ta Kwanaki Biyu a Jihar Katsina
A yau Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Katsina, The Nation ta rawaito.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ya yin wannan ziyarar shugaba Buhari zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Gwamna Aminu Masari ta aiwatar.