Wata mata da ta haifi jariri a gidan gyaran hali da ke Afao Ekiti a jihar Ekiti ta samu yanci yayinda wata kotu ta bada umarnin sallaamrta daga gidan gyaran hali.
A wani hukuncin da kotun daukaka kara da ke Ado Ekiti ta yanke a ranar 31 ga watan Agustan, ta jingine hukuncin da babban kotun tarayya da ke Ado Ekiti ta yanke na daure matar a gidan yari na tsawon shekara 4 sakamakon kamata da laifin sata.
Matar wacce take dauke da juna biyu a lokacin da aka daure ta, daga baya ta samu haifar jariri a cikin gidan yarin.
Matar gwamnan jihar Ekiti, Dakta Olayemi Oyebanji, ita ce ta shiga ta fita wajen nema wa matar yanci, ta kuma tabbatar da cewa za ta kula da walwalar yaririn da mahaifiyarsa.
Oyebanji tun da farko ta umarci sashin kula da jinsin mata da su tabbatar da samar da lauyoyin da za su daukaka kara kan shari’ar da ya kulle matar a gidan yari.
A WANI LABARIN KUMAGwamnatin Jahar Zamfara Ta Rufe Wasu Kasuwannin Shanu A Fadin Jahar
A hukuncin kotun daukaka kara da ke Ado Ekiti, ta jingine hukuncin babban kotun tarayya da ya daure matar a bisa dalilin cewa kotun ma bai da hurumin sauraron karar da ya shafi sata lura da sashi na 251 na kundun tsarin mulkin Nijeriya na 1999.
Kotun daukaka karar ta ce babban kotun jiya ce kawai ke da hurumin sauraron irin wannan kes din, don haka ta ce, ba da ta wata abun yi illa ta sallami matar daga gidan yari.