Wata mata mai karancin shekaru ta rasa ranta bayan ta lallaba saman wani ruwa mai gudana wanda aka rufe shi daga jama’a musamman don ta dauki selfie, LIB ta ruwaito.
Amanda Franco dos Santos, mai shekaru 26 ta fadi daga saman wani ruwa mai zuba da ke Santa Catarina a Brazil, inda ta zame ƙasa.
Duk da dai an dakatar da baƙi daga kai ziyara amma a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, Franco dos Santos daga garin Brazil na Mafra ta kai ziyara wurin.
Amanda da kawayenta biyu sun ki hakura da kin daukar hotunan don wallafawa a Instagram, hakan yasa su ka sauya hanyar shiga wurin.
Bayan na ne kawayenta biyu su ka kira ‘yan sanda don su isa Franco dos Santos daga nan su ka tsere da misalin karfe 4:50 na yamma. Nan da nan aka samu wasu ma’aikatan kashe gobara inda su ka taimaka su ka isa wurin.
Sun fara da bincike wurin. Amma ba su ganta ba a ranar farko, sai washegari ne su ka ganta duk ta samu raunuka sakamakon faduwar da tayi daga nesa.
KU KARANTA: Na kama matata dumu-dumu tana kwanciya da dan uwana, Miji ya nemi kotu ta raba auren
Wani dan kasuwa mai suna Justine Onu, ya bukaci wata kotu a Abuja ta warware aurensa da matarsa Joyce, bayan da aikata wani laifi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Onu ya bukaci warware auren nasu, bayan da ya kama matar sa na aikata lalata da dan’uwansa.
Ya bayyana kotun cewa ya gaza gane kan matar tasa tun ba yanzu ba, hakan ya sanya auren ya fice masa a rai kuma yake bukatar a kawo karshen auren.
Ya ce yanzu haka yana dauke da cutar hawan jini, sakamakon yawan samun matar sa da aikata abubuwan da basu kamata ba.