By Abbas Yakubu Yaura
Wata matar aure ‘yar shekara 25 mai suna Maryam Usman da ke unguwar Sheka a cikin birnin Kano, ta kashe kanta a ranar Alhamis din da ta gabata, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne yayin da marigayiyar ta tashi daga gidan aurenta ta koma gidan su domin samun kulawar iyayenta.
Kiyawa ya ce binciken farko ya nuna cewa marigayiyar ta kashe kanta ne ta hanyar yanke mata yatsa tare da raunata makogwaronta.
“A ranar 13 ga watan Janairu, mun samu wani rahoto mara dadi, cewa wata mata mai suna Maryam Usman ‘yar shekara 25 ta kashe kanta.
“Ta koma gidan danginta ne domin neman maganin rashin lafiyarta. Binciken da muka yi ya nuna cewa, kwatsam ta ciji mahaifinta, bayan da suka saka ta a daki, sai ta cije yatsanta, sannan ta karya tagar dakin.
“Mahaifin ya sanar da ‘yan sanda a yayin bincike cewa marigayiyar Maryam ta yi ta ihun cewa a bar ta ta je gidan mijinta don ya saketa ya bata takarda.
“Lokacin da muka samu kiran gaggawa, CP Samaila Shuaibu Dikko, ya aike da jami’anmu da mazaje wurin da lamarin ya faru, kuma an kai matar zuwa Asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda aka tabbatar da rasuwarta,” inji shi.