Ministar tsaftar muhalli ta Ghana, Cecilia Abena Dapaah, ta yi murabus bayan rahotannin da ke cewa ma’aikatanta sun gano tare da kwace wasu makudan kudaden gida da na kasashen waje daga gidanta, TVC News ta rawaito.
Dapaah ta yi kaurin suna ne bayan da aka tuhumi wasu tsoffin ma’aikatan gida biyu da laifin satar kudi da kayyakin ministar da mijinta tsakanin watan Yuli da Oktobar shekarar 2022.
KARANTA WANNAN: INEC Tana Ganawa Da Masu Sa ido, CSOs Domin Duba Zaben 2023
Masu gabatar da kara sun sanar da kotun cewa wadanda ake tuhumar sun yi amfani da kudin satar wajen siyan gidaje da mota, tare da baiwa ‘yan uwa wasu daga ciki.
Sai dai har yanzu dai ba su mayar da martani kan zargin ba.
Sai dai kuma, labaran jaridu game da dala miliyan 1, da dalar Amurka 300,000, da kuma miliyoyin cedi na gida da aka ce an sace daga gidan Dapaah, sun harzuka ‘yan kasar a kafafen sada zumunta tare da neman ta yi murabus.
Mutane da dama sun nuna shakku kan tushen irin wadannan makudan kudade a kasar da wasu wakilan gwamnatin shugaba Nana Akufo-Addo ke da hannu a badakalar cin hanci da rashawa.
“Duk da cewa zan iya bayyanawa a fili cewa wadannan alkaluma ba su dace da abin da ni da mijina muka kai wa ‘yan sanda rahoto ba, ina matukar sane da shigo da irin wadannan labaran kan wani a matsayi na,” Dapaah ta fada a cikin wasikar murabus din da ta yi wa shugaban kasa inda ta musanta aikata laifin.
“Ba na son wannan lamari ya zama ruwan dare ga gwamnati,” in ji ta, ta kara da cewa “ba shakka” za a wanke ta.
An amince da murabus din Dapaah, kuma fadar shugaban kasa ta yaba da aikinta ba tare da yin tsokaci kan ikirarin ba.
Akufo-Addo ya nada ta ministar tsaftar muhalli da albarkatun ruwa lokacin da ya hau mulki a shekarar 2017 kuma aka sake zabarta a 2021.
A wani labarin kuma,‘Yan Sanda Sun Haramtawa Masu Okada Sanya Takunkumin Hanci Da Hula
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta haramtawa masu sana’ar tuka baburan Achaba, da aka fi sani da masu tuka okada, sanya abin rufe fuska da hanci wato Takunkumi da huluna.
Inda ta gargadi mazauna garin da kada su hau baburan idan matukan suka sanya takunkumin ko hula.