Wata Sabuwa: Albashin ku na watan Janairu nawa ne – Wani Fasto ga mabiyan sa
Wani limamin cocin Najeriya Fasto Anosike ya shaidawa mabiya cocinsa cewa albashin watan Janairu na shi ne ba na coci ba.
Faston ya yi ikirarin cewa ba ya tsoron koma baya da caccaka, yana mai jaddada cewa abin da suke samu na farko na wannan shekarar nasa ne kawai.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ɗuminsa: Kotu ta baiwa tsohon Gwamnan CBN, Emefiele damar tafiya ƙasar waje
Ya ce idan mabiyansa suka dauke shi a matsayin ubansu na ruhaniya, to su ba shi kudin watan su na farko a wannan shekara.
Ya ci gaba da cewa irin wannan karramawa za ta kawo musu albarka.
A cikin wani faifan bidiyo, malamin ya yi ikirarin mayar da kudin idan mambobinsa ba su ba da shaida nan da tsakiyar shekara ba bayan sun ba shi gudummawar albashin watan Janairu.
“Albashin wannan wata shi ne na farko a wannan shekara, nawa ne ba na coci ba. Ina so in kalubalance ku, da ruhun ku, ba na jin tsoron kowa kuma ba na jin tsoron zargi da caccaka.
“Idan ka kira ni mahaifinka na ruhaniya, albashin wannan watan shine na farko na wannan shekara, nawa ne, ba na coci ba. Domin wannan bagade, domin wannan al’ajabi, na wannan kaso ne, wanda Allah ya shirya.
“Saboda jindadina ne, idan kun karrama ni da wannan albashin na shekararku ta farko, zuwa tsakiyar wannan shekarar, idan ba ku ba da shaida ba, ku dawo, zan mayar muku.
“Za ku ga abubuwan al’ajabi, alkawari da ruhuna, Bulus ya ce, ko da yake ba na nan, amma ina cikin ruhu. Na yanke hukunci, watakila ba zan iya ganin ku ba, amma ina kallo a cikin daula.
“A wannan shekara zan nuna muku asirai a cikin nassosi. Mutanen da suka yi amfani da su mutane ne masu mulki kuma Allah yana maido da daular.
A wani labarin kuma:NUJ ta yi Allah wadai da ƙawanyar ƴan sanda a wani gidan talabijin
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya reshen jihar Abia (NUJ) ta yi Allah wadai kan farmakin da jami’an ‘yan sanda suka yi wa gidan rediyo da talabijin na All Breaking News (ABN) Radio/TV, Umuahia.
Jami’an ‘yan sanda sun kama wani bako da ke bada gudunmawa a wani shiri kai tsaye yayin da lamarin ya faru.