Wata Sabuwa: An Samu Ɓullar Sabon Nau’in COVID-19 A Burtaniya
Hukumar Tsaron Lafiya ta Burtaniya, UKHSA, ranar Juma’a ta gano mutum na farko daya kamu da sabon nau’in cutar COVID-19 mai samfurin BA.2.86 a cikin kasar.
UKHSA a cikin wata sanarwa a shafinta na yanar gizo, UKHSA ta bayyana cewa an gano sabon nau’in COVID-19 a cikin wani mutum wanda ba shi da tarihin balaguro a cikin ƴan kwanakin nan.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wata Mata Ta Yiwa Mijinta Duka Saboda Ya Fita Da Daddare Ba Tare Da Ya Fada Mata Ba
Dr Meera Chand, Mataimakin Darakta na UKHSA ta ce “Muna sane da wanda da aka tabbatar ya kamu da cutar a Burtaniya. Za mu ba da ƙarin bayani nan gaba bayan kammala tantancewa.”
A ranar Alhamis, hukumomin lafiya na Amurka da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce suna sa ido sosai kan sabon nau’in Covid-19.
Ko da yake, a halin yanzu ba a san tasirin BA.2.86 ba kamar yadda WHO ta ayyana cutar a matsayin samfurin da ake cigaba da dubawa biyo bayan irin abubuwan da ke tattare da ita.
Hakanan an gano bambance-bambancen BA.2.86 a Denmark, Isra’ila da Amurka.
A wani labarin kuma:Masarautar Gudi Ta Jajantawa Sarkin Tikau Kan Rasuwar Madaki
Masarautar Gudi dake jihar Yobe ta jajantawa sarkin Tikau, Alhaji Muhammad Abubakar Ibn Grema kan rasuwar babban jigo a masarautar, Alhaji Musa Lawan (Madakin Tikau).
Sarkin Gudi, Alhaji Isah Bunuwo Ibn Madubu Khaji, wanda yayi jajen ta bakin Madakin Masarautar Gudin, Alhaji Muhammad Gadaka ya ce babu shakka anyi babban rashi wanda ya samar da gibi mai matukar girma ga iyalan sa, masarautar, Tikau da sauran al’uman jihar.