‘Yan Majalisun Jamhuriyar Benin sun kada kuri’ar amincewa da dokar zubar da ciki, wadda zata baiwa mata damar rabuwa da dantayin dake cikin su lokacin da suke bukata.
A karkashin sabuwar dokar, mata na iya zubar da cikin da bai wuce watanni 3 ba, idan zai yiwa rayuwar su illa ko kuma zai shafi harkar su ta karatu ko kuma aikin da suke ko wani bangare na rayuwar su.
Kafin wannan lokaci dai doka ta haramta zubar da ciki a Jamhuriyar Benin, muddin ba yana tattare da hadari ne ga rayuwar mai dauke da cikin ba, ko kuma wadda aka yiwa fyade ko wadda mahaifinta ko kuma ‘dan uwan ta ya mata ciki, ko kuma an gano dan tayin na da wata matsala.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace bayan tafka mahawara, musamman daga marasa goyan bayan dokar, daga karshe masu goyan bayan ta sun samu nasara.
Kasashen Afirka da dama sun haramta zubar da ciki, cikin su harda Congo-Brazzaville da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Djibouti da Masar da Guinea Bissau da kuma Senegal.
Ministan lafiyar Jamhuriyar Benin Benjamin Hounkpatin yace akalla mata kusan 200 ke mutuwa kowacce shekara sakamakon matsalar da ake fuskanta lokacin zubar da ciki.
Hounkpatin yace amince da sabuwar dokar zai karfafa gwuiwar mata da kuma kare lafiyar su, musamman wadanda basa bukatar daukar juna biyun.
Ministan yace akalla kashi 20 na matan dake mutuwa a kasar na rasuwa ne sakamakon zubar da ciki, kuma wannan na daga cikin dalilan da suka saka gwamnati daukar matakin yin sabuwar dokar.
Sai dai bangaren malaman addinin kasar na adawa da shirin, wanda suka ce na illa ga rayuwar dan tayi da kuma matar dake dauke da shi.