An Fille Kai tare da cire hannayen wata tsohuwa mai suna Iya Elekuru a garin Ile-ile na Jihar Osun, don yin asiri da shi.
Rahotanni sun bayyana cewa an yaudari tsohuwar ce mazauniyar garin Modakeke aka shigar da ita wani gida da suna siyan abincin siyarwar ta, inda daga bisani sa dai kwatsam aka samu labarin wannan aika-aika.
Kawo yanzu da muke baku wannan kabarin wadanda ake zargi da wannan mummunar ta’ada suka arce da kai da hannayen nata, to sai dai wasu Fusatattun Matasa sun kona gidan da aka gano gawar tata.
Kuma tuni Rundunar Yan Sandar Jihar ta bakin Kakakin ta Yemisi Opalola ta tabbatar da faruwar al’amarin inda ta ce a yanzu haka ta kaddamar da fara bincike kan lamarin.
Rundunar ta kuma ce za a baiwa yan uwan mamaciyar gawar ta don mata sutura.