Hukumar kula da sansanin ‘yan gudun hijira da ke Uhogua, kusa da Benin, ta ce wata da ba a san ko wacece ba ta jefar da wani jariri dan kwanaki biyu a cikin al’ummar.
Ko’odinetan sansanin Fasto Solomon Folorunsho ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Ya zama Dole Na Zama Shugaban Najeriya — Peter Obi
Folorunsho ya ce an gano jaririn ne a cikin wani dan jeji dake sansanin ta kofar shiga sansanin a ranar Juma’ar da misalin karfe 11 na safe.
Ya ce jaririn, wanda a halin yanzu yana karkashin kulawar lafiya a cibiyar kula da lafiya ta sansanin, wanda aka jefar da shi dauke da wani rubutun takarda.
“Mun gano jaririn mai kimanin kwana daya ko biyu a cikin jejin da ke kofar shiga sansanin.
“An jefar da jaririn tare da wani rubutu wanda ya karanta ‘don Allah a taimake ni in kula da shi. Ba zan iya kula da shi ba, domin ba ni da komai, kuma ba na son in kashe shi, don haka abinda ka bayar shi ne naka don Allah.
Ko’odinetan ya ce an kai rahoton ci gaban ga hukumomin da abin ya shafa da kuma hukumomin tsaro a jihar kamar ma’aikatar mata da ‘yan sanda da kuma hukumar tsaro ta DSS.
A halin da ake ciki, Folorunsho ya yi kira ga iyayen yaron da su kasance masu kwarin gwiwa su fito, inda ya kara da cewa yaro na bukatar shayarwa .
A cewarsa, “ina kira ga iyayen yaron da su fito kada su ji tsoro, idan ba don komai ba don a ba wa jariri nono, yayin da muke neman tallafi.
“Ko kuma mu hada kai mu samarwa (mahaifiyar yaron) hayar gida, a taimaka mata da abinci da sauran abubuwa, tunda ta ce dalilin da ya sa ta dauki matakin shi ne saboda ba za ta iya kula da yaron ba.
“Idan tana da tallafi, na tabbata, za ta iya kula da jaririn. Idan mace za ta kasance a can, za mu tallafa wa yaron.
“Amma idan babu wannan, a shirye muke mu kula da yaron da kuma horar da shi kamar sauran yara a nan, saboda wasu yaran da muke da su a nan an kawo su ne ‘yan ƙanana, kodayake wannan shi ne mafi ƙanƙanta.”
Ko’odinetan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su taimaka wa yaron da kayan jarirai, abinci da sauran abubuwa masu gina jiki.
“Yayin da muke kula da wannan yaron tare da ma’aikatan jinya da muke da su a nan da kuma ma’aikatanmu, muna kira ga ‘yan Najeriya masu kishi da su taimaka wa yaron.
“Saboda lallai muna bukatar taimako ta fuskar tufafin jarirai, abincin jarirai, da sauran abubuwa masu gina jiki da yaron ke bukata,” in ji shi.
Folorunsho ya ce tabbas iyayen yaron sun jefar da shi ne saboda kwarin gwiwar cewa sansanin na kula da duk jariran da ke hannunsu ne.
“Yadda muke kula da yara a nan, ina jin labarin yana ko’ina. Kowa ya san mu da yadda za mu iya kula da yaron.
“Muna tarbiyyantar da su da kyau ta fuskar tarbiyya, ilimi, kula da komai.
“Don haka na yi imani cewa ita wata ce ta san mu, ko kuma wani ya gaya mata game da mu,” in ji shi
A wani labarin kuma, Kotu Ta Daure Wani Basarken Gargajiya Tsawon Shekaru 10 A Gidan Yari
Wata kotun majistare da ke Osi a yankin karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, ta yanke wa wani basaraken gargajiya mai suna Ajagun Ode na Ode, Oba Adewale Sunday Boboye, hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa samunsa da laifin lalata bishiyoyin dabino da kayan abinci ba bisa ka’ida ba.
Tun da farko dai an tuhumi Oba Boboye da laifuka shida da suka shafi aikata barna.