Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a daren Lahadi ya tarbi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso zuwa Fatakwal, babban birnin jihar, gabanin kaddamar da titin cikin gida na Mgbutanwo a karamar hukumar Emohua ran Litinin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamna Wike ya gayyaci ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa kaddamar da ayyuka a jihar Kudu-maso-Kudu mai arzikin man fetur.
KARANTA ANAN: An Baiwa Ganduje da Mai Ɗakinsa Sarauta a Jihar Delta
Gwamnan na Ribas ya ce ya gayyaci ‘yan siyasan adawa su gudanar da kaddamar da ayyuka a jihar sa domin su gani da idon su su shaida wa ’yan jam’iyyarsu.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole a ranar Larabar da ta gabata ya kaddamar da gadar sama ta 8 a jihar da ke kan titin Ada George, daura da wani gida mai zaman kansa na Wike na Rumueprikom a cikin karamar hukumar Obio-Akpor.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya kuma kaddamar da gadar sama ta 9 a babbar mahadar Ikoku a ranar Alhamis.
Hakazalika, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da harabar makarantar Fatakwal na makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya a ranar Juma’a.
Watanni da watanni, Wike da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP da aka fi sani da G5 suna neman Iyorchia Ayu da ya yi murabus, suna masu cewa bai kamata ‘yan Arewa su zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa da kuma dan takarar shugaban kasa ba.
Sai dai kuma, Ayu, dan asalin jihar Benue, ya dage kan cewa ba zai sauka ba har sai karshen wa’adinsa na shekaru hudu, kamar yadda G5 suka bukaci yin murabus dinsa a matsayin wani sharadi na goyon bayan Atiku Abubakar, haifaffen Adamawa a zaben 2023.
Yayin da ba a ga Wike da abokansa sun yi wa Atiku kamfen ba, ba a san ko za su goyi bayan Bola Tinubu na jam’iyyar APC ko Obi ba a takarar neman kujerar Aso Rock wanda manazarta da masu lura da al’amura suka bayyana a matsayin tseren doki uku.
A wani labarin kuma, 2023: Kwankwaso Ya Gana Da ‘Yan Kabilar Yarabawa Ta Afenifere
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Lahadi ya gana da shugabannin kungiyar ‘yan kabilar Yarbawa ta New Afenifere, domin neman goyon baya gabanin babban zabe na 2023.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwankwaso ya yi alkawarin gudanar da mulki na bai daya wanda zai taba kowane bangare na kasar nan.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa,Tsohon gwamnan jihar Kano da ya yi wa’adi biyu, ya yi alkawarin cewa jam’iyyarsa za ta ceto kasar daga dukkan kalubale da kuma dora ta kan turbar ci gaba.