Kocin Barcelona, Xavi Hernandez, ya yi hasashen kasashen da zasu fafata a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta FIFA ta bana da kuma kungiyoyin fa zasu fafata a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai ta 2022-2023. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake yi a Qatar a halin yanzu na matakin wasan kusa da na karshe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ka Na Matsamun Zan Fasa Kwai— Dogara Ya Mayar Wa Wike Da Martani
Sifaniya za ta kara da Morocco sannan Portugal za ta kara da Switzerland a wasan zagaye na biyu na karshe a yau (Talata).
Da yake bayar da hasashen nasa, Sportskeeda ta ruwaito Xavi yana cewa, “Shin kuna hasashen wasan karshe na cin kofin duniya? To za ayi ne tsakanin Brazil Da Sifaniya.”
Dangane da batun gasar zakarun Nahiyar Turai kuwa, ya kara da cewa, “Shin kuna hasashen wasan karshe na gasar zakarun Turai? Yana da matukar wahala a iya hasashen, amma ina tunanin Bayern Munich ne za su kara Manchester City.”
A wani labarin kuma, Shugaba Ramaphosa Ya Firgita Kan Batun Tsigeshi Daga Mulki, Ya Wani Bukaci Taimako
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na kokarin dawo da kimarsa a siyasance sakamakon zarginsa da badakalar miliyoyin Dala a gonarsa sannan kuma ya yi rufa-rufa kan satar kudin. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ya kuma yi kira ga Mambobin jam’iyyarsa ta ANC mai mulkin kasar dake majalisar dokoki, da su mara masa baya, yayin da wasu manyan jami’an lauyoyinsa ke neman soke binciken da kwamitin kwararrun shari’a ke masa kan babbar badakalar data janwo cece kucen.
Wanda yake zargin Ramaphosa, shi ne tsohon jami’in leken asirin kasa Arthur Fraser.
Bayanan hakan na kunshe ne a cikin kalaman da ya yi wa jami’an tsaro, kuma an sanya su a cikin rahoton kwamitin, wanda majalisar za ta yi muhawara kan su a ranar Talata mai zuwa.
Mista Fraser ya yi zargin cewa wani makusancin Mr Ramaphosa, Bejani Chauke, ya kawo dalar Amurka masu yawa daga kasashen Saudi Arabiya, Masar, Morocco, da Equatorial Guinea, kuma ya kara da cewa, mataimakin ya boye kudaden ne a ciki gidansa.
Amma abun takaici shugaban kasa, da wasu yan fashi, da ake zargin sun yi aiki tare da wani ma’aikacin sa, waja sace abin da ake tunanin zai kai tsakanin dalar milliyan 4 kwatankwacin Fam Milliyan 3, zuwa dala Milliyan 8.
Sai dai Mr Ramaphosa ya musanta wannan Laifi, kuma kwamitin bincike karkashin jagorancin wani tsohon alkalin alkalan kasar ta Afrika ta Kudu, ya ce ba zai iya tabbatar zarge zargen ba, yayin da Shugaban yaki amincewa da shaidun da ke kunshe cikin kalaman Fraser.
Rahotanni sun bayyana cewa Mr Ramaphosa ya amince cewa an sace dala 580,000 a gonarsa a watan Fabrairun shekarar 2020