Yaƙi A Gaza: Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zargi Isra’ila da keta dokar jinƙai ta Duniya
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya zargi Isra’ila da keta dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa a harin da ta kai a Gaza.
Ya bayyana hakan ne a jiya Talata a lokacin da yake Jawabi ga mambobi 15 na kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a hedikwatar MDD dake birnin New York a yayin bikin ranar Majalisar Ɗinkin Duniya.
An nuna damuwa game da rikicin da ke faruwa a Gaza inda Isra’ila ta katse abinci da wutar lantarki.
Tun bayan harin da Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba Isra’ila ta fara kai munanan hare-hare ta sama da ta kasa a Gaza.
KARANTA NAN:Wani Ɗan Kasuwa ya maka Iyalan Marigayi Hassan Usman Katsina A Kotu, ya buƙaci Naira Miliyan 150
Shugabanin Amurkawa, da Turawa, da Jamusawa, da na Kanada da Italiya sun bukaci Isra’ila da ta bi dokokin ƙasa da ƙasa da kuma kare fararen hula tare da jaddada ‘yancin Isra’ila na kare kanta daga “ta’addanci”.
Guterres ya yi gargaɗin a ranar Talata cewa “babu wani ɓangare da ke cikin rikici da ya wuce dokar jin kai ta ƙasa da ƙasa.”
“Na damu matuƙa game da keta dokokin ƙasa da ƙasa da muke gani yana faruwa a Gaza,” in ji shi
Ya tuna cewa babu shakka ya yi Allah wadai da ayyukan ta’addanci na 7 ga Oktoba da Hamas ta yi a Isra’ila.
Babu wani abu da zai iya tabbatar da kashe-kashen da gangan, da kuma yin garkuwa da fararen hula – ko harba rokoki kan fararen hula.
Dole ne a bi da duk waɗanda aka yi garkuwa da su cikin mutuntaka kuma a sake su nan da nan ba tare da wani sharadi ba.
Guterres ya lura cewa halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya yana kara taɓarɓarewa cikin sa’a yana mai cewa yaƙin Gaza na ƙara kamari kuma yana da hatsarin yaduwa a duk faɗin yankin.
Rarrabar kan al’ummomi ne ya wargaza zaman lafiya, A muhimmin lokaci irin wannan yana da muhimmanci al’ummomin duniya su kasance a kan ka’idoji – farawa da ainihin ka’idar mutuntawa da kare fararen hula ”
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa, hare-haren da kungiyar Hamas ke kai wa ba ya faru ne a kan niyya ba.
Ya ce an shafe shekaru 56 ana mamayar Falasdinawa “Sun ga kasarsu ta ci gaba da cinyewa da matsuguni da kuma fama da tashin hankali;
tattalin arzikinsu ya tauye;
mutanensu da suka rasa matsugunansu an ruguza gidajensu, fatansu na samun mafita a siyasance ya ci tura”
Sai dai ya bayyana cewa koke-koken al’ummar Falasɗinu ba zai iya tabbatar da munanan hare-haren Hamas ba.
Ya ce hare-haren bama-bamai da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a zirin Gaza “matakin asarar rayukan fararen hula da lalata unguwanni na ci gaba da hauhawa kuma yana da matukar tayar da hankali.”