Yaƙi da cin hanci da rashawa ba shine kaɗai abinda Najeriya ta santa a gaba ba, har da ƙasar Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Joe Biden, kamar yadda Babban Jami’a a Amurka Claire Pierangelo ta bayyana.
Tace Gwamnatin Biden a shirye take domin bada goyon baya ga magance cin hanci, tare da inganta hanyoyin bincike akan masu cin hanci da zartar da hukunci ga masu cin hanci da hukumomi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dole Ne Cire Tallafin Man Fetur Jama’ar Kasa Su Amfana, Cewar Kungiyar Gwamnoni
Pierangelo ta bayyana haka a ranar Juma’a a yayinda Babbar Jami’ar, haɗin gwiwa da hukumar sasanci tsakanin addinai a Najeriya suka ƙaddamar da wani adireshi mai suna ReportMagoMago.com da aka zana domin shigo da ƴan ƙasa wajen yaƙi da cin hanci.
A cikin sanarwar da Temitayo Famutimi,mai kula da harkoki na jami’ar, ta bayyana cewa Pierangelo wannan adireshi zai baiwa iko ga ƴan ƙasa wajen kawo rahotannin cin hanci da rashawa.
Ta kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su bada himma wajen yaƙi da cin hanci, ta hanyar amfani da shafin na yanar gizo, wanda keda magance duk wata matsala ta cin hanci da miliyoyi ƴan Najeriya ke fuskanta.
“Cigaba da samun nasara a Najeriya ya dogara ga sabbin dabaru ga al’ada, tare da hana baiwa cin hanci ƙofa” inji ta.