Yaƙi: Rasha ta kai mummunan hari a babban birnin Ukraine, kyiv
Dakarun Rasha sun kai hari a Kyiv babban birnin Ukraine da jirage marasa matuka a safiyar Lahadi.
A cewar CNN, shaidu sun ji karar fashewar abubuwa akalla biyar amma har yanzu ba a tantance girman harin ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Koda An Gyara Matatun Man Fetur Ɗin Najeriya, Mai Ba Zai Sauko Ƙasa Da 200 – Dillalai
Rasha ta kai wani hari ta sama a cikin dare a cikin birnin yayin da aka ji karar fashewar wasu abubuwa a babban birnin Ukraine.
Harin wanda ya faru da sanyin safiyar Lahadi, an ce ya dauki tsawon awanni biyu ana kai harin.
An ga tarkacen jirage masu saukar ungulu na fadowa a wasu yankunan tsakiyar birnin.
Kafofin yada labaran Ukraine sun kuma nuna wasu motoci da suka lalace a harin.
Sai dai kawo yanzu ba a san girman harin ba, kuma ba a samu rahoton jikkata ba.
An kuma ce jiragen sun zo ne daga bangarori daban-daban’ a cewar jami’in soja
Magajin garin Kyiv ya ce mutum guda ya ji rauni a unguwar Podil kuma gobara ta tashi kusa da daya daga cikin wuraren shakatawa na birnin.
Serhiy Popko, shugaban hukumar soji ta birnin Kyiv, ya ce “jirage marasa matuƙa sun zo babban birnin kasar a rukuni kuma daga bangarori daban-daban.”
A wani labarin kuma:Koda An Gyara Matatun Man Fetur Ɗin Najeriya, Mai Ba Zai Sauko Ƙasa Da 200 – Dillalai
Kungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya ta ce ba zai yiwu farashin man fetur ya yi kasa da Naira 200 ba, ko da an gyara matatun mai.
Kungiyar ta lura da hakan ne biyo bayan wani rahoto da aka buga kwanan nan, inda kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya ta ce farashin man fetur zai fadi kasa da Naira 200 kan kowace lita idan matatun sun sake fara aiki.