A karshen makon da ya gabata Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi kira da a haramtawa ‘yan majalisar dokoki da ma’aikatan gwamnatin kasar tafiye-tafiye zuwa ketare. BBC ta ruwaito.
Museveni ya kara da cewa, haramtawa Jami’an Gwamnatin tafiye-tafiye zai taimaka wajan samu kudaden da za a aiki da su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kada Ku Zabi APC Da Wadanda Basu Da Sanin Makaman Aikin Shugabancin Najeriya — Atiku
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da wasu cibiyoyi a Cibiyar Man Fetur ta Uganda-Kigumba (UPIK) inda kasar ke da niyyar horar da kwararrun cikin gida kan hakar mai.
Uganda na fatan fara hako miliyoyin ganga mai a shekarar 2025 daga dimbin arzikin man da take da shi, sai dai shugaban bai ji dadin yadda har yanzu cibiyar horarwa ba ta kammalu ba saboda rashin kudi.
A cewar kafar yada labarai ta Daily Monitor a kasar, shugaba Museveni ya kuma bayar da shawarar a dakatar da duk wasu alawus-alawus na wasu jamai’an gwamnatin kasar.
A wani labarin kuma, Ya Kamata DSS Su Yi Gaggawan Cafke Gwamnan CBN — Falana
Wasu ƙwarararun Lauyoyi a Nijeriya masu riƙé da muƙamin (SAN) sun buƙaci gwamamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bi umurnin babbar Kotun Tarraya , da babbar Kotun Abuja waɗanda suka haramta mata ta, kamawa ko tsare Gwamnan babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Fitacen lauyan kare haƙkin bil Adama Femi Falana ya buƙaci Hukumar tsaro ta farin kaya DSS da ta ci gaba da ƙoƙarin da ta keyi na kama Emefiele bayan dawowarsa daga Nijeriya, inda ya bayyana cewa gwamnan babban Bankin Nijeriya, baya cikin waɗanda kundin tsarin mulkin na ƙasa ya baiwa rigar kariya