Yadda Ƴan sanda suka cafke wasu ɓarayin da ke fashi a gadar Neja ta biyu
Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta cafke wasu ‘yan fashi guda biyu da suke gudanar da aiki na fashi da makami a kan gadar Neja ta biyu.
Kwanan nan an lura da gadar a matsayin kogon ‘yan fashi, yayin da ‘yan fashin kuma suka yi amfani da damar wajen lalata wasu kayan aiki a sabuwar gadar da aka gina.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ina Son Yin Koyi da Okocha a Craven Cottage — Dan Wasa Iwobi
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), DSP Tochukwu Ikenga, ne ya bayyana kama ‘yan fashin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.
Ya ce: “Jami’an ‘yan sandan jihar Anambra da ke aiki da sashin Harbour a makon da ya gabata sun damke wasu ‘yan fashi guda biyu suna korar wasu mutanen da ba su ji ba gani ba a kan gadar Neja ta biyu.
“Rundunar ‘yan sandan sun sanya ido a kan ‘yan fashim inda ta kai musu farmaki inda suka cafke biyu daga cikin ‘yan ta’addan yayin da wasu suka gudu.
“Lokacin da aka bincika, an gano wasu wukake guda biyu da katin SIM biyar da aka cire daga wayoyin da aka sace a baya daga hannun wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 20 zuwa 22.
“Daya daga cikin wadanda ake zargin ya fito ne daga jihar Enugu, dayan kuma daga jihar Ebonyi.
“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Aderemi Adeoye ya yabawa rundunar ‘yan sandan bisa yadda suke taka-tsantsan da jajircewarsu wajen tunkarar ‘yan kungiyar.
“Ya ba da umarnin a gano masu katinan SIM din da aka kwato da nufin tattara shaidun samun nasarar gurfanar da wadanda ake zargin.
A wani labarin kuma:Kwankwaso Ne Kadai Zai Iya Fitar da NNPP daga Cikin Rikici – Masu Ruwa da Tsaki
Yayin da rikicin jam’iyyar, NNPP ke kara ta’azzara, masu ruwa da tsaki na ganin cewa Sanata Kwankwaso shi ne mafi cancantar magance takaddamar jam’iyya
Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanakin baya jam’iyyar ta tsunduma cikin rikici inda wani bangare ya dakatar da Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar