Yadda Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane uku
Biyo bayan mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama a ranar Asabar a unguwar Dakingari da ke karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, mutane uku sun rasa rayukansu.
Shugaban karamar hukumar Suru, Alhaji Muhammad Lawal Suru, ya ce baya ga mutuwar mutane uku, ambaliyar ta kuma lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta sanar da rufe wasu manyan kasuwannin shanu
Ya ce bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan da ke gangarowa daga tsaunukan da ke kewayen garin Dakingari ya taimaka wajen ambaliya.
Ya ce, “Sama da shekaru ashirin muna fama da ambaliyar ruwa lokacin da ake ruwan sama. Gwamnatocin baya na Nasamu Dakingari da Atiku Bagudu sun gina magudanan ruwa a garin domin magance matsalar amma hakan bai hana faruwar ambaliyar a duk shekara ba.”
A cewarsa, za a iya hana ambaliya idan za a iya gina shingen da mashigar ruwa a kewayen tsaunukan.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su daina kafa gine-gine a magudanar ruwa, da kuma zubar da shara ba gaira ba dalili.
A wani labarin kuma:Ƴan sanda sun ceto mutane ukun da aka yi garkuwa da su a Kaduna
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ce jami’anta sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a unguwar Kuriga Wussa da ke karamar hukumar Zariya.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansir Hassan ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jihar Kaduna.