Yadda wani sabon yamutsi ya hallaka babban limami da Ɗan Acaɓa a Filato
An kashe wani babban limami, Sani Idris da wani direban Okada, Muhammad Gambo a wani sabon hari da aka kai a karamar hukumar Bakkos ta jihar Filato.
Wannan mummunan lamari dai ya zo ne mako guda bayan an kashe mutane sama da 150 a wasu hare-hare da aka kai a kauyuka 23 a karamar hukumar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Har Yanzu Nine Shugaban Jam’iyya Na Jiha – Adams Ga PDP
A ranar Laraba, Garba Abdullahi, shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta Gan Allah, GAFDAN, ya tabbatar da harin.
Ya ce malamin da aka kashe shi ne babban limamin masallacin Juma’at da ke kauyen Ndun da ke gundumar Tangur a karamar hukumar Bokkos.
Da yake ba da labarin yadda lamarin ya faru, shugaban GAFDAN ya ce: “An kai wa babban limamin hari da kaninsa a ranar Litinin bayan da suka isa al’umma domin tattara wasu kayayyakinsu da suka rage a harin da aka kai kwanan nan inda aka kona gidajen mambobinmu.
“Don haka, sun je wurin ne don ganin ko za su iya karbo wasu kadarorinsu, amma sai aka kai musu hari ba zato ba tsammani. Maharan sun kashe limamin ne yayin da kanensa ya tsira da raunukan da aka yi masa na adduna.”
DAILY POST ta tuna cewa a jajibirin Kirsimeti wasu ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Bakkos da ke Filato, inda suka kashe daruruwan mutanen kauyen.
Lamarin da ya janyo fushin ‘yan Najeriya kan gazawar gwamnati wajen kare rayukan ‘yan kasar.
Sake faruwar hare-haren na zuwa ne duk da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara wani aiki na musamman