Wata matar aure mai ɗauke da juna biyu mai suna @natyfromboston a shafin TikTok ta bayyana wani bidiyo da ya nuna farin cikin da iyayenta suka ji yayin da suka samu labarin tana ɗauke da ciki.
A bayaninta, Naty tace mahaifanta sun jima suna dako na tsawon shekaru suna rokon ta samu ciki kuma ta haifa musu jikoki, Legit.ng ta rahoto.
KARANTA ANAN: Kotu Ta Hana EFCC Kwace Kaddarorin Gwamnan Matawalle
A bidiyon mai ban sha’awa, ta baiwa iyayenta wani ɗan karamin Akwati cike da kayan jarirai ta umarci su buɗe su gani.
Nan take bayan sun buɗe, mahaifiyar Naty ta fahimci abinda kayan dake cikin Akwati. Ke nufi, sai farin ciki ya baibaye fuskarta.
Mahaifin ya biyo bayan cikin farin ciki kana suka rungume juna yayin da hawaye ke kwaranya daga idanuwansu saboda tsantsar farin ciki da jin wannan kyakkyawan labari da suka jima suna dako.
Yadda mutane suka faɗi ra’ayoyinsu
Bcr yace:
“Lallai mama na cikin farin ciki, ji yadda ta ɗauki ɗaya daga kayan jaririn ta shinfiɗa kafaɗarta kai kace jaririn na ciki, ina taya ku murna.”
King.roajs yace:
“Jikoki wata ni’ima ce ga iyayen mu musamman idan komai ya tafi dai-dai, su maka aure su buya kuɗin sadaki da sauransu. Na so a ce iyayena na raye su gani da idonsu, ina da yakinin Babana sai ya ɗakko jirgi an tafi shagali.”
Favour Dumbiya tace:
“Gunin sha’awa hawayen farin ciki, farin cikin kowace Kaka bai wuce ta yi wasa da ‘yan jikokinta.”
Lord Paradise yace:
“Ko babu Miji wasu iyalan suna nuna farin cikinsu.”
A wani labarin kuma Majalissar Zartaswar PDP Ce Zata Yanke Hukunci Kan Matsayar Ayu, Yayin Da Kwamitin BoT Ya Mika Rahotansa
Kwamitin musamman da Jam’iyar PDP ta kafa da kwamitin amintattu na jam’iyyar , ya mika rahoton da aka dade ana jira kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ga majalisar zartaswar jam’iyar na kasa , don yanken hukuncin da ya ‘dace’.
Mukaddashin shugaban Kwamitin amittaun jam’iyar na kasa , Sanata Adolphus Wabara, ya yi kira ga “dukkan shugabannin jam’iyyar da su daidaita kalamansu da aiki.”