Yadda wata mata ta daba wa ‘yar shekara 12 wuka a Rivers
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta ce mutanenta sun kama wata mata mai suna Abigail da laifin daba wa wata yarinya ‘yar shekara 12 wuka tare da barin wuka a jikinta a garin Rumuodara da ke karamar hukumar Ohio/Akpor a ranar Asabar.
Yarinyar, mai suna Oluebube, tana zaune ne a cikin harabar gidan tare da matar, mai shekaru 30, lokacin da yarinyar ta nuna rashin jin dadi kan wata karamar matsala.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda Manoma A Kano Suka Koka Kan Tsadar Takin Zamani
Da take bayyana wa manema labarai faruwar lamarin a garin Fatakwal a ranar Asabar, ‘yar uwar yarinyar mai suna Olucho, ta ce matar ta aikata hakan ne saboda kuskuren ‘yar uwarta ta buge ta da ruwa a kofar gidansu.
Ta ce, “Yar uwata tana wanke faranti a waje. Matar (Abigail) ta je ta debo ruwa.
“Saboda layinmu duhu ne, wanda ke ciki zai iya ganin wani a waje, amma wanda ke waje ba ya iya ganin mutumin a ciki.
“Matar ta tsaya da ruwanta, amma ba ta ce wa ‘yar’uwata kada ta zo da tukunyar don gudun kutsawa cikinta ba.
“Don haka ‘yar’uwata, ba tare da sani ba, ta shiga da tukunyar, ta shiga cikin matar, su biyun suka fadi.
“Matar yanzu ta fara dukan kanwata. Wasu makwabta suka fara rokon matar cewa kuskure ne, amma matar ta ki.”
Olucho ta ce matar ta umurci ‘yar uwarta da ta share ruwan da ya zubo, ita kuma ta ci gaba da diban ruwan, kuma ta amince.
“Saboda haka ta koma dibar wani ruwa, yayin da kanwata ta ci gaba da wanke kwanonin, daga baya ta dauki tsintsiya don share ruwan.
A wani labarin kuma:
Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa bai da masaniyar cewa iyayensa na da arziki a lokacin da yake girma.
Ya ce kawai ya san cewa mahaifinsa, Cif Adedeji Adeleke, mai arziki ne tun yana dan shekara 13.