Yadda Za’a Shawo Kan Matsalar Hauhawar Farashin Man Fetur A Najeriya – Yan Kasuwa
A cike da takaicin da ya biyo bayan tashin farashin man fetur zuwa Naira 617 a kowace lita, babban jami’in gudanarwa na kamfanin Emadeb Energy Service Limited, Debo Olujimi, ya ce tace man fetur a cikin gida shi ne kadai mafita mai dorewa da zata kawo maslaha ga hauhawar farashin man fetur.
A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, Olujimi ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da Depot na tauraron dan adam na Ijegun ranar Laraba a Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamna Radda Ya Sake Nada Kwamishinonin Masari 3 Da Sabbi 17
Olujimi ya bayyana cewa karin farashin man fetur zai ci gaba da cutar da ‘yan Najeriya matukar ba a karfafa tace man a cikin gida ba.
Ya koka da yadda ake ci gaba da dogaro da dalar Amurka wajen shigo da man fetur a kasar.
“ Sanin kowa ne cewa karin farashin man fetur ya yi matukar matsin lamba ga ‘yan Najeriya, wanda duk mun fahimta.
“Hanya daya tilo da za a magance kalubalen da ke gudana ita ce gwamnati ta karfafa aikin tace a cikin gida,” in ji shi.
A wani labarin kuma:Tabbas Yan Najeriya Za Su Yi Murna, Su Yi Rawa Idan Aka Soke Zaben Ka – PDP Ga Tinubu
Jam’iyyar PDP ta ce ‘yan Najeriya za su fito kan tituna cikin murna idan kotu ta soke nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben 2023.
Pedro Obaseki, Daraktan Dabaru da Bincike na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP (PCC) ne ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba.