Shugaban kungiyar malaman Kwalejin Fasaha ta kasa (ASUP) Anderson Eziebe, ya ce yajin aikin da suke yi yanzu haka, zai iya kaiwa shekara mai zuwa suna yi.
Eziebe ya bayyana hakan a yau Talata, yayin da yake wa mambobin kungiyar karin haske, wanda suka gudanar da taron a Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin tarayya dake Ilaro, a jihar Ogun.
Ya kara da cewa kusan shekara guda suka cimma matsaya da Gwamnatin tarayya kan yarjejeniyar fahimtar juna, amma har kawo yanzu ta gaza aiwatar da ita a aikace.
Yanzu dai ASUP ta na yajin aikin gargadi ne na tsawon makwanni biyu, sakamakon yadda kudaden ariyas Ɗinsu suka makale tsawon watanni 10, baya ga rashin albashi da sauran wasu bukatunsu.
Ezeibe ya kara da cewa a shekarar 2021, sun tafi yajin watanni uku kan wannan matsala, gwamnati ta bukaci su janye tare da yi musu alkawari, amma kawo yanzu ta gaza cika alkawarin da ta dauka.
Daga nan sai ya bukaci mambobin kungiyar da su shiryawa yajin aiki mai tsawo anan gaba, domin kuwa babu alamar zasu janye nan kusa.