Yajin Aikin ASUU: Ƙungiyar Ɗalibai Ta Nemi Buhari Ya Kori Ministan Ilimi
Kungiyar dalibai ta Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori ministan ilimi Mallam Adamu Adamu bisa abin da suka bayyana a matsayin rashin iya aiki.
Shugaban kungiyar daliban Sunday Asefon, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce Ministan ya kara tabbatar da rashin sanin makamar aiki da gazawarsa wajen warware yajin aikin da malaman jami’o’in ke yi a karkashin kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU makonni biyu bayan shugaban ya umarce shi da yin hakan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Majalisar Neja sun buƙaci Gwamna Bello ya dakatar da Zaɓen Ƙananan Hukumomi
Ya ce: “Saboda haka ya tabbatar da cewa Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu bai da karfin tafiyar da irin wannan muhimmiyar ma’aikatar ta ilimi.”
“Hakan ya isa a saka ayar tambaya game da cancantar nada shi a matsayin ministan ilimi tun da farko. Gaba daya rashin tausayinsa da tausayawa halin da daliban Najeriya ke ciki ya yi yawa.”
“Tun da malam Adamu ya zama minista kungiyar ASUU ta tafi yajin aiki na kusan watanni 18 a dunkule, kuma tsarin ilimi na manyan makarantunmu ya durkushe a karkashin kulawarsa.
“Don haka ya zama wajibi a yi kira ga shugaban kasa da ya gaggauta sauke shi daga aikinsa na ma’aikatar tare da kawo hazikin mutum wanda zai ceto ilimi.”
Shugaban kungiyar daliban ya ce bacin rai na iya tilasta wa daliban su fara cewa “Adamu-Must Go” kamar yadda suka yi na “Ali-Must-Go”.