Yajin Aikin ASUU: Ku koma aji don cigaba da Karatu – Buhari ya roki Malaman Jami’a
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin kira ga kungiyar malaman jami’o’in da ke yajin aiki da su dawo ajujuwa.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar kasar na bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Manoma 14 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Taraba, Da Dama Sun Bata
Ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da biya bukatun malamai a cikin iyakokin “karancin albarkatun”.
Ya ce “Ina amfani da wannan bikin ranar ‘yancin kai ne domin nanata kirana ga kungiyar malaman jami’o’in da ke yajin aikin da su dawo ajujuwa tare da ba su tabbacin magance matsalolin da suke fuskanta a cikin iyakacin karancin albarkatun da ake da su.
“Wannan gwamnatin ta samu ci gaba mai inganci wajen gyara wadannan al’amuran da aka shafe sama da shekaru 11 ana yi.”
“Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada-hadar albarkatun kasa da kasa da kasa wajen samar da tallafin ilimi domin tabbatar da cewa ‘yan kasarmu sun samu ilimi mai inganci tare da samun kwanciyar hankali a sana’o’i daban-daban ganin cewa ilimi shi ne kan gaba wajen tabbatar da ci gaban tattalin arziki.
Yanzu dai ba labari bane cewa malaman jami’o’in Najeriya sun shiga yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabreru saboda rashin warware matsalolin da gwamnatin tarayya ke fuskanta.
A wani labarin kuma: Najeriya Na Da Abubuwan Sambarka Yayin Cika Shekaru 62—- Gwamnan Gombe
A jiya ne gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce ‘yan Najeriya na da abubuwan da yakamata su nuna matukar farin cikin su akai da murnar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai duk da kalubalen da kasar nan ke fuskanta.
A wani sako na bikin cikar Najeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai da kuma bikin cika shekaru 26 da kafa jihar, Gwamna Yahaya ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yanke kauna amma su ci gaba da sa rai a yunkurin gina kasar nan..