Yajin Aikin ASUU: NANS za ta toshe filin jirgin sama na Fatakwal, babbar hanyar Calabar-Itu
Kungiyar dalibai ta kasa (NANS), shiyyar Kudu maso Kudu, ta yi barazanar toshe filin jirgin sama na Portharcourt, babbar titin Calabar Itu da kuma rufe muhimman ababen more rayuwa a shiyyar idan har kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta cigaba da yajin aiki.
Jami’in Ƙungiyar na Shiyyar Kudu-maso-Kudu, NANS ZONE B, Kings Tamarapreye ne ya bayyana hakan a karshen makon da ya gabata yayin wani taron manema labarai a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dubu Ta Cika: Yan sanda Sun Kama Masu Saffarar Aburusai Daga Legas Zuwa Katsina
Da yake kira ga ASUU da ta bi umarnin kotu ta janye yajin aikin na watanni 8, NANS ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kuma amince da bukatun ASUU na cewar dalibai sun fi shan wahala.
Tamarapreye ya yi barazanar cewa idan ba a yi la’akari da bukatun NANS ba, mataki na gaba zai iya zama mafi muni fiye da zanga-zangar EndSARS.
Sanarwar ta kara da cewa, “A matsayinmu na shugabannin NANS ZONE B, muna so mu sake jaddada kudurinmu na komawar daliban Najeriya zuwa Jami’o’in karatu daban-daban.
“Muna ba da kuri’ar amincewa ga gwamnatin Kwamared Usman Barambu domin yayi aiki wajen dinke barakar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
“Muna sake jaddada matsayarmu gaba daya ta hanyar yin kira ga kungiyar da ta mutunta umarnin bude cibiyoyin kamar yadda muke kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan bukatun ASUU.
“A bisa labarin cewa a wannan shiyya ta musamman (NANS Zone B, Kudu-maso-Kudu), mun gudanar da zanga-zanga da dama don ganin yadda za mu mayar da dalibai makaranta saboda babban dalilin da ya sa aka zabe mu shugabanni shi ne ba da fifiko ga jin dadin dalibai.
“Abin takaici ne cewa watanni takwas yanzu daliban Najeriya na nan a gida. Ya bayyana cewa mun toshe hanyoyin Akwa Ibom da Jihar Kuros Riba tare da hadin kai.
“Akwai takardar da aka rufe don wayar da kan al’umma kuma har yanzu tana kan hanya. Kamar yadda muke kira ga ASUU da su saurari umarnin kotu su koma makaranta, idan suka gaza, to za mu hada kai mu rufe kasar baki daya saboda gwamnatin tarayya ta yi sakaci a harkar ilimi a kasar nan.
“Dukkanmu mun san cewa ilimi a kasar nan ba shi da kudi kuma ba za mu nade hannunmu ba, lokaci ya yi da za mu dauki kaddararmu a hannunmu. A wannan yankin Kudu-maso-Kudu, za mu toshe filin jirgin sama na Portharcourt, tare da toshe babbar hanyar Calabar-Itu da sauran ababen more rayuwa.
A wani labarin kuma: Ku yi Addu’ar Allah ya kawo ƙarshen Ambaliyar Ruwa, tattalin arziki – Gwamna Buni ya roki shugabannin addini
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi kira ga malaman addini da su yi addu’a domin ci gaba da zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da malaman addinin Musulunci da na Kirista a Damaturu babban birnin jihar Yobe.