Gwamnatin Jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya ta umarci ma’aikatan lafiya da ke yajin aiki a jihar da su koma bakin aiki ko kuma ta kore su daga aikin nasu.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ambato kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Mista Charles Udoh yana bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Mista Udoh ya ce yajin aikin da likitocin ke yi a ƙarƙashin ƙungiyarsu mai suna Joint Health Workers Union (JOHESU) “na cike da manufofi na siyasa kuma sam ba ya kan tsari”.
Ya ƙara da cewa: “Buƙatar da suka gabatar ta a biya su kashi 50 cikin 100 na albashinsu a matsayin fansar hatsarin da suke shiga a irin wannan lokaci na matsin tattalin arziki babu tunani a ciki.”
Kwamishinan ya ce ana ta yabon ƙoƙarin da gwamnatinsu take yi game da lafiya a Najeriya, “saboda haka gwamnati na ganin wannan yajin aiki ba ya kan doka”.