Yakin da ake yi a Ukraine da hauhawar farashin kayayyaki ya jefa karin yara miliyan hudu a gabashin Turai da tsakiyar Asiya cikin talauci. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta bayyana kahan a cikin wani rahoto da ta fitar a yau Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mun Cimma Ayyuka Da Bukatun ‘Yan Najeriya — Buhari
Alkaluman, wanda ke wakiltar karuwar kashi 19 cikin 100 tun daga shekarar 2021, ya nuna cewa yara suna daukar nauyi mafi girma sanadiyyar rikicin
Binciken ya hada da bayanai daga kasashe 22 na yankin nahiyar.
Tasirin yakin ya kasance mai tsanani musamman ga yara a kasashwn Rasha da Ukraine.
A cewar binciken, A kasar Rasha, ƙarin yara miliyan 2.8 na rayuwa a gidajen dake fama da talauci.
Yayij da A Ukraine, ƙarin yara rabin miliyan suna rayuwa cikin talauci, sai Romania da ta samu ƙarin yara 110,000 da suke rayuwa cikin talauci, kamar yadda binciken ya nuna
Hukumar UNICEF ta yi gargadin cewa karuwan na iya haifar da karin yara 4,500 da ke mutuwa kafin cikarsu shekara daya da haihuwa.
Daraktan shiyya na Turai da tsakiyar Asiya Afshan Khan ya ce illar tattalin arzikin da yakin ke fuakanta na yin mummunar illa ga yara.
Binciken ya kuma yi nuni da cewa, daya daga cikin yara uku da aka haifa kuma suka taso cikin talauci, za su yi rayuwa cikin talauci, wanda hakan zai haifar da karin wahalhalu da a tsakanin al’umma.
Da yake magana kan hanyar da za bi domin dakile ci gaban lamarin, Khan Afshan ya ce, akwai bukatar karewa da fadada tallafin zamantakewa ga iyalai masu rauni kafin lamarin ya yi kamari.
A WNAI LABARIN KUMA: Kama Dan Takarar Sanatan Jam’iyyar Labour Aka Yi, Ba Sace Shi Ba – ‘Yan Sanda
Rundunar ‘yan sanda a Ebonyi, ta bayyana cewa “karya ne” batun da ake zargin an sace Linus Okorie, dan takarar kujerar Sanatan Ebonyi ta Kudu a jam’iyyar Labour a jihar.
Ya bayyana labarin da ake zarginsa da yin garkuwa da Mista Linus Okorie a matsayin na karya