Kwana hudu da rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta yi ikirarin cewa ta kama wasu ‘yan fashi da makami uku da ke da hannu wajen yin fashi da makami da yi wa daliban Makarantar Koyon Fasaha ta Gateway da ke Sapaade fyade, an sake kai wa daliban hari, inda daya daga cikinsu ya rasa ransa.
A harin na fashin, wasu dalibai tara kuma sun samu raunuka a harbin bindiga,harrin na baya-bayan nan ya zo ne mako guda bayan daliban makarantar suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da fashi da fyade da ‘yan barandan suka yi wa daliban makarantar.
Karanta nanBago Yayi Ta’aziya Ga Iyalan Tsohon Shugaban Kungiyar Kwadago Ta Jahar Neja
An tattaro cewa daliban da ke zaune a otal-otal din da ke Ode, Ipara da Isara, wadanda ke makwabtaka da Sapaade, galibin ‘yan fashin ne suka rutsa da su.
Bayan zanga-zangar da daliban suka yi a ranar Talatar da ta gabata, hukumar ta rufe makarantar na tsawon kwanaki uku domin dawo da zaman lafiya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abiodun Alamutu, ya kuma yi wata ganawa da shugabannin daliban a kan tashin hankalin da ya barke tsakanin al’ummar daliban.
Kwanaki ‘yan sanda sun ce sun cafke uku daga cikin ‘yan kungiyar da ke dauke da makamai,sai dai wadanda ake zargin ‘yan fashine sun koma yankunan da ke fama da rikici da sanyin safiyar Asabar inda suka far wa daliban.
A wani faifan bidiyo da aka dauka na harin da aka yi a Instagram, wakilinmu ya ga yadda kofofi suka farfashe, tagogi da katanga cike da harsasai.
A wani labarin kumaAbdulsamad BUA Ya Ki Karbar Tayin Zama Mamba A Kwamitin Kudi Na Jam’iyar APC
Daya daga cikin malaman, wanda bai so a buga sunansa ba saboda munin yanayin da lamarin ya faru, ya bayyana lamarin a matsayin “aiki ne da aka shirya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola, bai amsa kira da sakon da wakilinmu ya yi masa ba kamar dai yadda ya zuwa lokacin da aka buga labarin.
Shugaban hulda da jama’a na cibiyar, Adedayo Folorunsho, ya ki cewa komai kan harin,sai dai ta ce ya kamata a bar jami’an tsaro su yi aikinsu.