An harbe wasu ‘yan sandan biyar da wasu fararen hula uku a unguwar Gatikawa da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
Yan sandan an ce sun fito aiki na musamman ne daga Kano.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:35 na yammacin ranar Laraba, inda ‘yan bindiga sama da 300 suka far wa al’ummar garin inda suka fara harbe-harbe ba don tsorata mazauna yankin.
Daya daga cikin majiyar ta ce ‘yan bindigar wadanda ke rike da makamai masu sarrafa kansu da kuma hawa kan babura, suna bi gida-gida suna kwashe duk wani abu mai daraja da suka hada da kudi da kayan abinci.
Ya ce mazauna yankin da dama kuma sun jikkata musamman wadanda suka yi yunkurin tserewa.
Kana Ya ce mazauna yankin sun firgita bayan harin, kuma wasu mutane sun koma garuruwan da ke makwabtaka da su saboda fargabar sake kai wani hari.
Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wata guda da ‘yan bindiga ke kashe jami’an ‘yan sanda.
Idan ba a manta ba, ko A ranar 5 ga Yuli, 2022, wasu ‘yan bindiga sun kashe babban jami’in ‘yan sanda mai kula da karamar hukumar Dutsinma, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Aminu Umar, tare da wani dan sanda daya da wasu fararen hula.
A kokarin neman martaninsa da aka aike masa da sakon kartakkwana, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya rubuta cewa, “Gaskiya an kashe ‘yan sanda biyar daga Kano da ke aiki na musamman a Kankara da wasu mutanen kauyen Gatakawa uku.”
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda, ya mikawa iyalai da makusantan ‘yan sandan da suka rasu a madadin sufeto-Janar na ‘yan sandan da suka mutu kudi Naiar milliyan 14.6.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah ya fitar, ta ce gabatar da cak din na cikin shirin inshorar jin dadin iyalin yan sanda da sefeto janar ya kirkiro da ake baiwa iyalan jami’an ‘yan sanda da suka rasu a yayin aiki.