Wasu miyagun mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe wani jami’in ‘yan banga mai suna Malam Bakwai a kauyen Rimawa da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto.
Haka kuma sun raunata wani mutum guda kafin su yi awon gaba da wani dan gidan dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Goronyo a majalisar dokokin jihar Sokoto mai shekaru 18.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Banki a Najeriya Ya Haramta Wa Ma’aikata Musulmi Zuwa Sallar Jumu’a
Daily Trust ta tattaro cewa, an kai harin ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Laraba.
Shugaban karamar hukumar, Abdulwahab Goronyo, yayin da yake tabbatar da harin ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 4 na yamma.
A cewarsa, sun zo ne a kan babura daban-daban, kowannensu yana dauke da mutane uku dauke da muggan makamai.
“Ni da shugaban jam’iyyar PDP na jihar muna cikin garin Goronyo, muna jajantawa iyalan wadanda suka rasu lokacin da aka sanar dani harin, nan da nan na tara jami’an tsaro zuwa yankin amma ‘yan fashin sun tafi tare da yaron kafin isowar su. Haka kuma sun kashe dan kungiyar ‘yan banga guda daya tare da raunata wani mutum guda,” inji shi.
Majiyar Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa yaron yana cikin kauyen tare da mahaifiyarsa a lokacin da aka kai harin amma ta tsira da ranta.
Dan majalisar, Faruk Ahmadu Rimawa, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi waya a daren jiya amma ba su nemi wata bukata ba.
A wani labarin kuma, Gwamna Yahaya Bello Ya Fusata, ya baiwa Ɗangote Awanni 48 ya kulle Kamfanin sa
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayar da umarnin rufe kamfanin siminti na Obajana cikin sa’o’i 48.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, a makon jiya ne majalisar dokokin jihar Kogi ta zartar da kuduri na rufe kamfanin, biyo bayan gazawar Aliko Dangote na gayyatar da akayi masa.