An yi artabu a tsakanin ɓangarori biyu na ‘yan bindiga a kauyen Illela da ke karamar hukumar Safana ta Katsina, lamarin da ya yi sanadin rayuka da dama baya inda wasu kuma suka jikkata. Rikicin ya kaure ne tsakanin ɓangaren Mani Sarki da kuma Dankarami a sansanin Abu Rada, kamar yadda majiyarmu ta labarto.
Majiyoyi sun shaida cewa rikicin ya biyo bayan nadama da Sarki ya yi da kuma amincewa da afuwan gwamnati lamarin da ya sa ake masa kallon barazana da tafka rikici a kansa a sansanonin da ke dazukan yankin.