Daga: Abbas Yakubu Yaura
A jihar Kaduna, an kashe tsohon sakataren karamar hukumar Birnin-Gwari, Abubakar Muhammad Aliyu (Mai Yalo) da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
An yi garkuwa da Mai Yalo a gonarsa kimanin makonni 3 da suka gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/ba-zan-huta-ba-har-sai-na-ga-yan-najeriya-sun-sami-sauki-inji-shugaba-buhari/
Shugaban kungiyar masu ci gaba da masarautar Birnin Gwari (BEPU), Kasim Ishaq Kasai a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce ‘yan bindigar sun karbi kudin fansa amma sun kashe tsohon Sakataren kimanin kwanaki 11 da suka gabata.
“An ba mu labarin rasuwarsa a jiya, Alhamis, ta hannun kaninsa da ya tsere daga hannun ‘yan fashin.
” A cewar ‘yan uwa da abokan arziki, za a gudanar da Sallar jana’izar sa a ranar Asabar 10 ga watan Zul-Hijjah, 1443 dai dai da (9 ga watan Yuli, 2022) a filin Idi na kungiyar Izala, kusa da Base Airforce, titi Funtua, Birnin Gwari, Jihar Kaduna bayan Sallar Eid el-Kabeer.
“Wadanda ba za su iya zama a Birnin Gwari a lokacin ba, za su iya yi masa addu’ar samun lafiya a duk inda suke,” inji shi.
Al’ummomin masarautar Birnin-Gwari dai sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan, duk da cewa tun daga lokacin da jama’ar yankin suka kaura daga wuraren da suka fito zuwa wasu wurare masu tsaro.
A Wani Labarin Kuma Dr Sadiq Amali Malami a Sashen Nazarin Zaman ta kewa na Jami’ar Tarayya ta Jigawa, ya bayyana cewar sai da ya gano za’a kai hari a gidan yarin Kuje.
A lokacin da yake jawabi akan harin a gidan Talabijin na Channels a cikin shirin Sunrise Daily a ranar Alhamis, Dr Amali yace ya rubuta wa Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola, akan kaiwa wurin hari.
Ƴan bindiga da aka yi amanna cewa ƴan Ta’adda ne, a ɗaruruwan su, sun kai hari a gidan yarin a daren ranar Talata.
Maharan sun yi amfani da Bam domin samun shiga can cikin gidan da kuma ta hanyar katangar gidan.
Kimanin Fursunoni 879 suka tsere daga gidan yarin a lokacin kai harin, inda ake kyautata zaton 70 daga cikin su mambobin Ƙungiyar Boko Haram ne.
Masana Harkokin Tsaro sun ce idan har ba’a ɗauki mataki ba daga Hukumomi ba, to za’a cigaba da kai harin.
“Ina da Kyakkyawar alaƙa da Ministan Cikin Gida da Kwanturola-Janar akan yawaitar kai hare-hare a gidan yari a Ƙasar.
“Naga wannan. Kuma wannan bashi ne karo na farko ba da lamarin ya faru, kuma abin baƙin ciki ne ba lallai wannan shine na ƙarshe ba.
“A lokacin da suke rage yawan mutane a lokacin cutar Covid-19, na shawarci Ministan Cikin Gida akan matakan da zasu ɗauka, da kuma illolin da rage yawan yake dashi.
“To idan Fursunonin daka saki suka haɗa kai da wasu a cikin Al’umma suka dawo domin sakin ƴan uwan su dake garƙame.
“Naga harin na zuwa, kuma ya ɗauki mataki, amma matakan tsaron sun yi kaɗan.