An hallaka mutane biyu, yayin da wasu uku suka jikkata lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai hari a wata Cocin Celestial da ke Felele, Lokoja a jihar Kogi.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a bayan gidan mai na NNPC Mega da ke Felele.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Wani Sashe Na Kalaman Atiku
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun far wa cocin inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba.
An kara samun labarin cewa mutane biyu ne suka mutu nan take, yayin da wasu da dama kuma suka yi tururuwa domin tsira da rayukansu.
Wadanda suka jikkata a halin yanzu suna karbar kulawar likitoci a cibiyar kula da lafiya ta tarayya FMC dake Lokoja.
Wani ganau ya ce, “da suka shiga cikin harabar cocin, sai suka fara harbin kowa, Yanzu na je na ɓuya a cikin gonar rogo. Abin da na gani jiya ya kasance kamar wasan kwaikwayo a cikin fim. Kogi ba shi da lafiya”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Ovye Aya ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar DAILY POST a safiyar ranar Litinin.
A cewarsa, ’yan bindiga sun mamaye Cocin inda suka fara harbi kan masu ibada.
“Abin takaici ne da jami’an ‘yan sanda na B Division Felele suka samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wani cocin Celestial da ke bayan gidan mai na NNPC, suka fara harbe-harbe.”
“An tabbatar da mutuwar mutane biyu a asibitin, yayin da uku ke samun kulawar likitoci.”
“Kwamishanan ‘yan sanda ya tura jami’an mu, kuma ya umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke gudanar da bincike, da ya fara bincike domin gano musabbabin harin da nufin kamo wadanda suka kai harin,” inji shi.
A wani labarin kuma, Ambaliyar Ruwa: Ku Taimakawa Bayelsa, Da Sauran Jihohi – Buhari Ya Ummarci Hukumomin Bada Agajin Gaggawa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda ambaliyar ruwa ta afku a Bayelsa da sauran jihohin Najeriya.
Sannan shugaban ya koka da yadda ambaliyar ta yi barna a Jihohi 33 a fadin kasar nan.