Wasu ‘yan bindiga sun sake kashe wasu mutane biyu a wurin hakar ma’adanai a karamar hukumar Jos ta Arewa na jihar Filato.
Rahotanni na nuna cewa wadanda aka kashen matasa ne, inda suka je wurin hakar ma’adinan da ke unguwar Yelwa- Zangam a safiyar ranar Talata, sai ‘yan bindigar suka far wa matasan, inda suka kashe biyu daga cikinsu nan take yayin da wasu suka tsere.
Idan za’a iya tunawa, Al’ummar yankin Dong da ke yankin karamar hukumar sun gudanar da zanga-zanga a watan jiya bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe wasu matasa hudu a wurin da ake hakar ma’adinai a yankin.
Shugaban Kungiyar Cigaban Al’umar Anaguta, Sunday Bunu ya tabbatar wa da jaridar PUNCH kashe-kashen na baya-bayan nan a Jos a ranar Talata
Bunu ya ce “Muna wani taro da kwamishinan yawon bude ido na jihar sai aka kira ni, a na fadamun labari kan kisan.
“Daga abin da aka gaya min, wasu Fulani sun je wata makaranta a unguwar don yin kiwo da shanunsu amma ‘yan banga sun ce ba sa barin shanu su yi kiwo a wurin.” Inji shi
“Don haka, dan banga ya kori shanun daga makarantar. A yayin da shanun ke gudu, sai suka garzaya zuwa wajen da ake hakar ma’adanai, inda suka iske wasu matasan mu da suka fita da safe suke gudanar da ayyukan hakar ma’adanai a cikin al’umma.
“Wadancan matasan ba su san dalilin da ya sa shanun ke gudu ba, ba kuma su ne suka kori shanun dake kiwo a makarantar ba.
“Amma kafin ku sani, wasu Fulani da suka ga shanun sun gudu sun fito daga daji suka far wa matasan da ke aiki a wurin hakar ma’adanai ba tare da sanin dalilin ba.
“Abin takaici, sun yi nasarar kashe biyu daga cikin matasan yayin da wasu suka yi nasarar tserewa.”
Sai dai jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, wakilin nata yakasa ji ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, Ubah Ogaba, yayin da aka tuntubi shi ta wayar salula.
A lokacin da yake jawabi ga mazauna yankin Yelwa- Zangam a watan Agustan shekarar da ta gabata a ziyarar da suka kai bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane sama da 30, Gwamna Simon Lalong ya yi alkawarin kafa ofishin ‘yan sanda a cikin al’ummar da za ta dakile kai hare-hare a kan jama’a amma har yanzu gwamnan bai yi nasara ba wajan cika alkawarin.