Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar ranar Asabar, sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Adavi da ke jihar Kogi, inda suka kashe ‘yan sanda uku.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi (PPRO), William Ovye Aya ne, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja ranar Asabar.
Ya ce, “Rundunar ‘yan sandan ta samu rahoton afkuwar lamarin da ya faru a ofishin ‘yan sanda na Adavi, inda wasu ‘yan ta’adda suka far wa ofishin daga wani bangare suna harbe-harbe, amma jami’an da ke bakin aiki da jami’an Quick Response Unit da ke gudanar da ayyuka na musamman suka fatattake su. a karamar hukumar.”
Ya ce rundunar ta rasa jami’anta uku a yayin fafatawar da ‘yan bindigar yayin da ‘yan bindigar suka gudu da raunukan harbin bindiga saboda sun kasa samun damar shiga ofishin.
Aya ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Edward Egbuka, ya tura tawagar ‘yan sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya, yayin da suke bin sahun ‘yan fashin da nufin kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Rundunar ta yi kira ga al’ummar Adavi da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su da su sanya ido tare da kai rahoton duk wanda aka gani da raunin harsashi ga ‘yan sanda ko kuma jami’an tsaro na kusa da su.
A wani labari Kuma na daban
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya shaida wa tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido cewa abin takaici ne ba a tuntube shi ba kafin a zabe shi a matsayin daya daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar PDP da dattawan Arewa suka yi.
Lamido ya caccaki dattawan PDP na Arewa kan zaben Mohammed da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa na yarjejeniya a jam’iyyar.
Kamar yadda jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito a baya, dattawan Arewa sun gana a gidan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida inda suka yanke shawara a kan Mohammed da Saraki a matsayin wadanda aka tsayar bisa tsarin yarjejeniya bayan kammala tattaunawa.
Wannan shawarar dai ba ta yiwa Lamido dadi ba, wanda ya caccaki ta, ya ce dattawan Arewa da suka yi zaben ba sa magana ga ‘yan PDP a Arewa.
Sai dai Mohammed a martanin da ya mayar kan kalaman Lamido, ya ce yana da hakkin jin ra’ayinsa, inda ya kara da cewa ba a tuntubi tsohon Gwamnan ba yana nufin ba a tuntubi sauran ‘ya’yan jam’iyyar kafin amincewar ba kenan.
Da yake jawabi ga manema labarai a Bauchi a ranar Asabar din da ta gabata, Gwamnan ya ce, “Mutane na iya daukar hakan a matsayin wani abin da aka yi tasiri.
“Ina matukar girmama Alhaji Sule Lamido a matsayin sa na tsohon Gwamna kuma wanda yake jagorantar tsaffin gwamnoni.Ya cancanci ra’ayinsa.
“Abin takaici ne idan ba a shawarce shi ba ko kuma ba a tuntube shi ba amma tabbas, ba shi kadai ba ne a Arewacin Najeriya.