Wani mumunan fashin banki da aka yi a garin Ikere Ekiti na jihar Ekiti a ranar Laraba da yamma, rahotanni sun ce an kashe mutane biyar ciki har da jami’an tsaro biyu na Amotekun.
DAILY POST ta samu labarin cewa ‘yan fashin da suka sanya abin rufe fuska, sun afkawa bankunan kasuwanci da ke kan babbar hanyar garin inda suka bude wuta domin shiga harabar bankunan.
Karanta nanMatar Da Ta Hukunta Diyar Kishiyarta Da Wuta A Zamfara Za Ta Fuskanci Hukunci
Shedun gani da ido sun ce ‘yan fashin sun ajiye kansu a wurare masu mahimmanci inda suka yi harbi ba kakkautawa har na tsawon sa’a guda, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi a tsakanin mazauna yankin.
Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun samu harbin bindigar ‘yan fashin ne a lokacin da suke kokarin tsira da rayuwarsu.
Wakilinmu ya tattaro cewa ’yan fashin da suka rufe fuska, kimanin ashirin, sun shiga garin ne da misalin karfe 4:15 na yamma inda suka yi wa bankunan Odo Oja da Oke-osun fashi a lokaci guda.
Kamar yadda majiyar ta bayyana, sun fara kai hari ne kan kwamandan Ikere na Amotekun Corps da ke kan titin Ise, inda aka ce sun harbe wasu jami’an tsaro kafin su far wa bankunan.
‘Yan fashi da makami sun karya kofofin tsaron bankunan da taimakon dynamite, inda suka yi awon gaba da wasu makudan kudade da ba a tantance ba.
Sai dai kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu an kasa samunsa har zuwa lokacin mika wannan rahoton, saboda ba a amsa kiran waya da sakonnin wayar salula da dama.
A wani labarin kumaDa Ɗuminsa: Tinubu ya amince da fitar da malaman manyan makarantu daga tsarin IPPIS
A halin da ake ciki kuma, a wata tattaunawa ta wayar tarho, Ogoga na Ikere Ekiti, Oba Adejimi Alagbado ya bayyana kaduwarsa game da lamarin fashin.
Ya ce abin takaici ne ‘yan fashi da makami sun gudanar da aikin na tsawon mintuna da dama ba tare da wata tangarda ba, inda suka tsere duk da kasancewar shingayen binciken sojoji da rundunar ‘yan sanda a garin.
Oba Alagbado ya ce ya tattauna da jami’an tsaro kan lamarin, kuma dole ne a kama wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su gaban kuliya.