Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun sake kai hari a garin Maru, hedikwatar karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da hudu, ciki har da wani malami na Kwalejin Ilimi ta Jihar (COE).
A cewar wani mazaunin yankin, Usman Ibrahim, ‘yan bindigar sun kai farmaki garin Maru a daren ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu hudu, ciki har da Nasiru Mohammed Anka, malami a kwalejin ilimi ta Maru.
Karanta nanRundunar ‘Yan Sanda Ta Bayarda Umarnin Rarraba Motoci Masu Sulke Ga Jahohi Uku
’Yan ta’addan sun shigo garin ne da manyan makamai kuma suka fara harbe-harbe. Daga baya kuma sai suka koma gida gida, inda suka yi awon gaba da mutane hudu.
Sun kuma bude wuta kan wasu da suka yi kokarin tserewa,sun kashe mutane biyu tare da raunata wasu da dama yayin samamen.
A cewar wani mazaunin garin, Isiaku, harin da aka kai garin Maru a ranar Asabar da ta gabata shi ne irinsa na hudu a cikin wata daya kacal, kuma ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran hukumomin da abin ya shafa da su dauki kwararan matakai don shawo kan wannan mummunan lamari.
A wani labarin kumaFG ta Shirya Samar da Rundunar ‘Yan Sanda Ta Musamman Kan Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
Yan ta’addan sun kai hari garin, duk da cewa hedkwatar karamar hukuma ce kuma kusa da hanyar Gusau zuwa Sokoto. A makon jiya ne suka kai hari garin.
Duk kokarin da manema labarai suka yi don jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya ci tura, domin bai amsa kiran waya ba.