Yan bindiga sun yi Garkuwa da Hakimin kauyen Banye na karamar hukumar Charanchi dake jihar Katsina.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta gano cewa, an sace hakimin kauyen, Alhaji Bishir Gide Banye ne, tare da wani Dalibin Makarantar Sakandare da Yan bindigan suka azabtar dashi.
Wani mazaunin garin, wanda ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa,, ya tabbatar da cewa, maharan dauke da muggan makamai sun mamaye garin ne a daren ranar Juma’ar data gabata, sannan suka tafi kai tsaye zuwa fadar hakimin inda suka yi garkuwa da shi.
Banye ya ce, duk da yake a ƙaramar hukumar Charanchi an rufe hanyar sadarwa na waya, yanayin da ya ba maharan damar gudanar da satar ba tare da ƙalubale ba, saboda mazauna garin ba za su iya tuntubar jami’an tsaro ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun Ceto wasu Yan gidan Sarauta a Jihar Kwara
Wannan shine karo na biyu da aka sace wani hakimin kauye a yankin, inda tun da fari aka yi garkuwa da hakimin garin Barkiya da ke karamar hukumar Kurfi.
Sai dai yayi sa’ar samun ceto, yayin da aka sanar da jami’an tsaro sannan suka bi sawun masu garkuwa da mutanen.
Da aka tuntube shi don tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce, rahoton bai kai ga hedikwatar rundunar ba, amma ya yi alkawarin ganowa da komawa ga Manema Labarai.
Koyaya, bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.