Wasu Bata gari da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da basaraken yankin Bukpe da ke Kwali na Babban Birnin Tarayya Abuja, Hassan Shamidozhi da wasu mutane hudu.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren Laraba lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye fadar basaraken.
Shugaban sashen yada labarai a sakatariyar majalisar karamar hukumar Kwali, Emmanuel Habila, ya tabbatarwa da gidan talabijin na Channels TV lamarin a ranar Alhamis.
A cewarsa, ‘yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS a halin yanzu suna kan bin diddigin masu garkuwa da mutane domin ganin an kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su.
Habila ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da sarkin ke hutu a fadarsa.
Da Jaridar DAILY POST ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh ta ce za ta yi bincike kuma ta koma ga manema labarai..