By Ishaq Dabai
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun sace tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja.
An yi garkuwa da Ewuga, wanda ya taba zama Sanata inda kuma a kayi garkuwa dashi a yammacin ranar Talata a jihar Filato.
Tsohon Sanatan, wanda ya wakilci gundumar Sanatan Nasarawa ta Arewa daga shekarar 2011 zuwa2015, yana kan hanyar sa ta dawowa gida lokacin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da shi.
An yi garkuwa da shi ne a ranar da aka kashe mijin tsohon Ministan Yada Labarai Farfesa Dora Akunyili, Dakta Chike Akunyili a jihar Anambra.