Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya yi Allah-wadai da harin da sojoji suka kai ta sama wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Martanin Sani ya biyo bayan tabbacin da rundunar sojin Najeriya ta yi na cewa ita ce ke da alhakin harin da aka kai ranar Lahadi.
Karanta nanYan Sanda Sun Gano Maboyar Yan Bindiga A Adamawa,Sun Harbe Biyu
Ya ce kamata ya yi a jefa wadannan bama-bamai kan ‘yan ta’adda ba farar hula ba.
DAILY POST ta ruwaito cewar wani jirgi mai saukar ungulu mara matuki ya kai harin bama-bamai a wasu sassan al’umma, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba a daidai lokacin da mutanen kauyen ke gudanar da bukukuwan Mauludi na tunawa da haihuwar Annabi Muhammad.
Wani rahoto daga kauyen Kaduna da aka jefa bama-bamai kan mabiya addinin ya nuna cewa sama da mutane 150 ne suka mutu.
Mummunan aiki ne sojojin Nijeriya suka yi,domin ya kamata a jefa wadannan bama-bamai kan ‘yan ta’adda ba farar hula ba,” Sani ya rubuta a shafinsa na X ranar Litinin.
A wani labarin kumaGwamnatin Tarayya Ta Biya Tarar Naira Miliyan 52 Domin Sakin Fursunoni 399 A Kaduna
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta samu bayanai kan harin, inda ta bayyana cewa rundunar sojin kasar na ci gaba da gudanar da ayyukanta na yaki da ‘yan ta’adda amma ba da gangan tayi abin ba.
Gwamnati ta ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin da ya dabaibaye harin ta sama.
Ta kuma ba da umarnin kwashe wadanda suka jikkata cikin gaggawa zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko domin samun kulawar gaggawa.