Yan bindigan da su kayi garkuwa da mutane kusan 60 a jihar Kaduna na neman buhunan shinkafa da man gyada domin ciyar da wadanda abin ya shafa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka kai hari cocin Emmanuel Baptist da ke Kakau Daji a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna a mako daya da ya gabata.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigan sun yi barazanar idan ba a samar mu da kayan abinci ba, Kuma wadanda abun shafa ka iya fuskantar matsanancin Yunwa..
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN a Kaduna, Reverend John Hayab, ya shaida wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa masu garkuwa da mutane na neman makudan kudade a matsayin kudin fansa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 3 sun Mutu yayin da Gobara ta tashi a Abuja
Wani dan unguwar da ‘yan uwansu na cikin wadanda aka sace ya shaida wa Majiyarmu a ranar Asabar cewa ‘yan bindigar sun yi kiran ne da daddare ne a ranar Alhamis domin neman abinci daga jama’a.
Kwamishinan tsaron da kula da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya tabbatar da yin garkuwa da mutanen a wata sanarwa kwana guda bayan faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun kuma kashe wani mai ibada a yayin harin.
A wani Labarin Kuma na daban.
Hukumar yada labarai ta kasa ta gargadi gidajen yada labarai da su guji yada labaran da ka iya kawo cikas ga hadin kan kasar, yayin da zaben Anambra zai gudana a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Zaben Anambra: NBC ta yi gargadi game da yada shirye-shiryen da ka iya kawo cikas ga hadin kan Najeriya, wanda Darakta Janar na hukumar ta NBC, Balarabe Ilelah, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Ilelah ya umurci duk masu yada labaran zaben gwamna da su bi ka’idojin zabe da aka tanada a kundin tsarin yada labaran Najeriya.
Sanarwar ta ci gaba da bayyana wasu daga cikin dokokin da masu watsa shirye-shirye zasu bi, inda ta kara da cewa bai kamata a yi hasashen sakamakon zabe ba bisa ka’ida ba a dandalinsu.
Dokar ta kara da cewa, “5.3.3 (j) tabbatar da cewa watsa yakin neman zabe na bangaranci, jingle, sanarwa da duk wani nau’i na tantance jam’iyyar siyasa ko alama yana karewa sa’o’i ashirin da hudu kafin ranar zabe, kar a yi amfani da duk wata ƙuri’ar da aka samu a wurin jefa ƙuri’a ko daga rumfunan zaɓe don tsara ko hasashen yiwuwar ɗan takara;
Kazalika “5.3.3 (k) ta mika sakamakon zabe ko bayyana wanda ya yi nasara kamar yadda jami’in zabe mai izini na zaben ya sanar.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hukumar tace masu watsa shirye-shiryen da suka saba wa tanade-tanaden za su fuskanci hukunci mai tsanani.