By Abbas Yakubu Yaura
An harbe wani mutum mai suna Saheed Lawal dan shekara 40 da kuma wani mai babur a wurare daban-daban a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a karshen mako.
Yayin da aka kashe Lawal a gidansa da ke shiyyar Elelubo, a unguwar Bako, Apata, daura da hanyar Ibadan zuwa Abeokuta, an kashe direban babur din ne a unguwar Barika da ke Agbowo, Ibadan.
Jaridar Aminiya ta tattaro cewa Lawal, ma’aikacin (POS) ya dawo gida ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Asabar, inda ya je masallacin karfe 7 na yamma, amma ya gamu da ajalinsa bayan ya dawo gida.
A cewar wani mazaunin unguwar, ‘yan fashin sun zo ne a kan babur, inda biyu daga cikinsu suka je gidan marigayin, suka buga kofa suka ce ya ba su kudi.
Sai dai kuma”An harbe shi bayan bude kofa,” in ji shi.
Majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta kara da cewa “Daya daga cikin ‘yan fashin ya harbe shi a kirjinsa a kusa da wajen. Matarsa ba ta san cewa mijinta ya rasu ba, tana rokon su kar su kashe shi kamar yadda suke neman kudin da ke cikin gidan da ta ba su,” ya kara da cewa.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan fashin sun tsere akan babur bayan tafka ta’asar.
An yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Shugaban kungiyar masu gidajen, Mutiu Adewunmi, ya shaida wa wakilinmu cewa, an kai rahoton faruwar lamarin zuwa ga ofishin ‘yan sanda na Omi-Adio da misalin karfe 9 na ranar.
“Muna zargin wasu ’yan ta’adda ne a unguwarmu kuma mun kira ‘yan sanda amma suka ce mu tsare al’ummarmu da kanmu.
“Sun yi ikirarin ba a kai rahoton faruwar lamarin a ofishin su ba duk da cewa suna wurin da aka yi taron har ma sun dauki hotuna a baya.
‘Yan sanda a ofishin ‘yan sanda na Omi-Adio ba su yin wani abu don kare mu ba, Muna bukatar goyon bayan Sufeto Janar na ‘yan sanda musamman kwamishiniyar ‘yan sandan jihar Oyo, Misis Ngozi Onadeko, domin su taimaka mana,” inji shi.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kisan da aka yi wa direban babur din da ya faru da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar ya jefa mazauna yankin wadanda yawancin su daliban jami’ar Ibadan ne cikin firgici.
Wani mazaunin garin mai suna Gabriel, ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata cewa ‘yan fashin sun harbe mahayin okada a kusa da wajen.
Sannan ya ce mahayin okada yana tafiya ne da wani fasinja, sai ‘yan bindigar suka tare shi a mahadar da ke gaban kofar jami’ar UI ta biyu kuma suka yi yunkurin kwace masa babur din.
“Maiyin okada bai so su tafi da babur ba kuma ana cikin haka sai fasinjan ya yi tsalle ya gudu ya bar wurin.
“Da yake jin cewa juriyar mahayin okada na iya jefa su cikin hatsari, sai daya daga cikinsu ya fito da bindiga ya harbe shi a kai,” in ji shi.